Ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta ba da labari a yau cewa, ya zuwa yanzu, yawan tasoshin sigina ta 5G da Sin ta kafa ya zarce miliyan 4.1, matakin da ya gaggauta habaka wannan fasaha zuwa kauyuka, don tabbatar da cewa, siginar 5G ta kai ga isa dukkan kauyuka.
A halin yanzu, fasahar 5G na shiga manyan nau’o’in harkokin tattalin arzikin al’ummar Sinawa guda 80, yayin da kuma ake ci gaba da kokarin amfani da ita a mabanbantan fannoni masu zurfi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp