Ma’aikatar ilimi ta kasar Sin, ta ce kasar ce kan gaba a duniya, a fannin samar da tsarin ilimin koyar da sana’o’i mafi girma tsakanin kasashen duniya. Ma’aikatar ta shaidawa manema labarai na kafar CMG hakan ne, yayin wani taron ‘yan jarida da ta shirya a baya bayan nan.
Bayanai daga ma’aikatar ilimin sun nuna cewa, ya zuwa shekarar 2023, adadin makarantun koyar da sana’o’i dake kasar Sin ya kai 11,133, makarantun da suka horas da dalibai kusan miliyan 35.
- A Karon Farko Adadin Motoci Masu Aiki Da Sabon Makamashi Da Kasar Sin Ke Kerawa Duk Shekara Ya Zarce Miliyan 10
- Nijeriya Na Buƙatar Maki 3 Yau Domin Samun Gurbi A Gasar Ƙasashen Afrika
Bugu da kari, kasar Sin ta samar da wani sahihin tsari na gudanar da hadin gwiwar kasa da kasa a fannin bunkasa ilimin koyar da sana’o’i, ta kuma aiwatar da ayyuka da dama a karkashin hadin gwiwarta da kasashe da yankunan nahiyar Afirka, da tsakiyar Asiya, da kudu maso gabashin Asiya da Turai.
A halin yanzu, kasar Sin ta kafa cibiyoyin koyar da sana’o’i na “Luban” sama da 30, a yankuna daban daban karkashin hadin gwiwa da kasashen Asiya, da Turai da Afirka, cibiyoyin da suka horas da dabilai kusan 10,000, a fannonin ilimin daban daban, da dalibai kusan 31,000 a fannin koyar da sana’o’i. (Mai fassara: Saminu Alhassan)