Kakakin ma’aikatar hadin gwiwa da sauran kasashe da tabbatar da ci gaba ta kasar Sin Xu Wei, ya furta a yau Litinin cewa, domin amsa kiran da MDD ta yi, da sasanta yanayin jin kai a zirin Gaza, kasar Sin ta riga ta samar da agajin jin kai na gaggawa, ga ofishin MDD mai kula da kai dauki ga Falasdinawa, gami da hukumar ikon al’ummar Falasdinawa, don biyan bukatun jama’ar zirin Gaza a fannonin abinci, da aikin jinya, da samun mafaka, da dai sauransu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp