Yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi kira ga Amurka, da ta yi bayani game da batun balan-balan nata dake ratsa yankunan samaniyar kasashe daban daban.
Wang Wanbin wanda ya yi kiran yayin taron manema labaru da aka gudanar, ya ce tun daga watan Mayun shekarar bara, Amurka ta tura balan-balan da dama zuwa sassan duniya. A cikin su akwai wadanda suka ratsa yankuna mallakin kasar Sin sau fiye da 10, ba tare da samun izini ba.
Game da batun balan-balan na farar hula na Sin, wanda ya shiga samaniyar Amurka bisa kuskure, sau da dama Sin ta yi Amurka bayani, amma Amurkan ba ta yi bayani game da batun balan-balan nata ba, a hannu guda kuma ta zargi Sin da fitar da bayanai ba na gaskiya ba.
Game da hakan, Wang Wenbin ya yi nuna da cewa, ya kamata Amurka ta yi la’akari da wannan yanayi, ta dakatar da zargin kasar Sin ba tare da hujja ba, da daina bayar da labarai marasa tushe ga Amurkawa, da sauran sassan kasa da kasa.
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin na adawa da matakin Amurka, na sakawa kamfanoni, da hukumomin Sin takunkumi bisa wancan zargi, kuma Sin za ta mayar da martani kan hukumomi, da kungiyoyin Amurka masu haifar da illa ga ikon mallaka, da tsaron kasar Sin, don kare moriyar ta. (Zainab)