Alkaluman hukumar lura da albarkatun al’umma, da inganta rayuwar jama’a ta kasar Sin, sun nuna cewa kasar ta samar da karin adadin sabbin guraben ayyukan yi na birane har miliyan 6.98 a rabin farko na shekarar bana.
Alkaluman da hukumar ta fitar a Talatar nan, sun nuna cewa a watan Yunin bana, mizanin rashin ayyukan yi a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, yayin da gaba daya aka samu daidaito a fannin samun ayyukan yi.
Har ila yau, kasar Sin na fatan samar da sabbin guraben ayyukan yi har sama da miliyan 12 a birane a duk shekara. Tare da burin ci gaba da wanzar da mizanin rashin aikin yi na birane kan kaso kimanin 5.5 bisa dari a shekarar nan ta bana. (Saminu Alhassan)