Wani mai magana da yawun ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ya ce Sin ta kara sunayen wasu kamfanonin kasar Amurka 7, cikin jerin sassan da ba za a iya amincewa da su ba, bisa la’akari da dokoki, da ka’idoji masu nasaba da hakan. Kazalika, an fayyace jerin takunkuman da za a aiwatar kan wadannan kamfanoni.
Jami’in ya ce, kamfanonin 7 sun yi watsi da matukar adawar Sin game da sayar da makamai, da musayar fasahohi tare da bangaren da Sin din ba ta amincewa, wanda hakan ya yi matukar keta hurumin ikon mulkin kai, da tsaro da moriyar kasar Sin.
- Xi Ya Zanta Da Babban Jagoran Vietnam Da Shugaban Sri Lanka
- Hauhawar Farashin Kayayyaki Ya Kai Kashi 34.80 A Disamban 2024 – NBS
Ya ce, har kullum kasar Sin na yin takatsantsan, wajen tantance kamfanonin da take sakawa a wannan jeri, kuma sassan kasashen waje kalilan da suke kokarin illata tsaron kasar Sin ne kadai ke shiga cikin jerin sunayen.
Daga nan sai jami’in ya yi kira ga kamfanonin waje, dake gudanar da harkokinsu bisa doka da su kwantar da hankulansu, a gabar da gwamnatin Sin din ke ci gaba da yin maraba da kamfanonin waje, su zuba jarinsu a kasar, tare da alkawarin samarwa kamfanonin waje masu bin doka da yanayi madaidaici, na adalci, kuma abun dogaro, wanda zai ba su damar gudanar da harkokinsu yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)