Ma’aikatar kula da dazuzzuka da yankunan dausayi ta kasar Sin ko NFGA, ta sanar da karin wurare 22, da aka shigar cikin yankunan dausayi masu matukar muhimmanci na kasar Sin. Ma’aikatar ta ce da wannan kari yanzu jimillar irin wadannan wurare dake cikin kasar Sin ya kai 80.
Sabbin wuraren da aka kara na nuni ga kwazon kasar Sin, na ci gaba da karfafa kare yankunan dausayi a shekarun baya-bayan nan, ciki har da aiwatar da dokar musamman ta farko, mai nasaba da kare yankunan dausayi, wanda hakan muhimmin mataki ne a ayyukan kare muhallin halittu na kasar.
Ya zuwa yanzu, kasar Sin na da yankunan dausayi 82 da aka sanya cikin jadawalin kasa da kasa na yankunan dausayi mai muhimmanci, da wasu 22 dake cikin jadawalin kasa da kasa na birane masu dausayi. A wannan fanni, kasar Sin ta kara, ko farfado da fadin yankunan dausayi da ya kai sama da hekta miliyan daya a sassa daban daban na kasar.
A nan gaba kuma, NFGA ta ce za ta ci gaba da ingiza ayyukan farfado da yankunan dausayi, da sanya ido kan kokarin da ake yi wajen inganta yanayi, da daidaito a tsarin wanzar da muhallin halittu a yankunan dausayin. (Saminu Alhassan)