Darektan hukumar kula da makamashi ta kasa da kasa Fatih Birol ya bayyanawa wakilin babban gidan rediyo da talebijin na kasar Sin wato CMG a yayin taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na shekarar 2024 a jiya cewa, Sin ce a kan gaba a duniya a fannin raya makamashi mai tsabta, don haka ya kamata sauran kasashe su koyi fasahohi masu kyau da kasar Sin ta samu a wannan fanni.
Bayanai sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2022, yawan makamashin da ba na kwal da gas da man fetul ba da kasar Sin ta yi amfani da shi, ya kai kashi 17.5 cikin dari, kana yawan wutar lantarki da ta samar ta na’urori masu yin amfani da makamashin da za a iya sabuntawa ya kai kiloWatt biliyan 1 da miliyan 213. Kana yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi a kasar Sin ya kai miliyan 20 da dubu 410.
- Xi Ya Taya Felix Antoine Tshisekedi Murnar Lashe Zaben Shugaban Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo
- Kasar Sin Ta Harba Kumbon Dakon Kaya Domin Aikewa Da Kayayyaki Ga Tashar Sararin Samaniya
Game da nasarorin da Sin ta samu a fannin makamashi mai tsabta kuwa, Birol ya bayyana cewa, Sin tana kokarin sa kaimi ga samun babban ci gaba a wannan fanni a duniya. Ba ma kawai Sin tana inganta amfani da makamashi mai tsabta a cikin gida ba, har ma ta samar da shirinta na raya irin wannan makamashi ga al’ummomin kasa da kasa.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana rage farashin amfani da fasahohi marasa gurbata muhalli a duniya, ta hanyar ba da damar yin amfani da makamashi mai tsafta a wurare daban daban masu dimbin yawa, tare da taimakawa yin amfani da makamashin da za a iya sabuntawa a fadin duniya. Wannan babbar gudunmawa ce da kasar Sin ta samar wa duniya, in ji Malam Birol. (Zainab Zhang)