A yau Alhamis ne ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya kira wani taro don tattauna rahoton ayyukan gwamnatin kasar, wanda majalisar gudanarwar kasar ke shirya gabatarwa, ga taro karo na biyu na babban taron jama’ar kasar Sin karo na 14. Kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya jagoranci taron.
A gun taron, an bayyana cewa, a cikin shekarar da ta gabata, an cimma burin raya tattalin arziki da al’umma a kasar Sin, inda aka tabbatar da samun bunkasuwa mai inganci yadda ya kamata.
A shekarar bana kuma, Sin za ta karfafa da inganta yanayi mai kyau na farfadowar tattalin arziki, ta yadda za a habaka bunkasuwar tattalin arziki mai inganci. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp