A gaisuwar murnar sabuwar shekara da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekarun da suka gabata, ya sha ambaton kalmar “gwagwarmaya”, Daga “aiki tukuru don cimma buri”, zuwa “farin ciki na tafe bayan yin aiki tukuru”, wannan ya shaida cewa, yin kokari ya kasance karfin neman samun ci gaba, kana ya taimaka wajen samun kyakkyawar makoma, kuma tsari ne mai wahala. Akwai bukatar yin kokari a yayin da ake neman samun ci gaba a sabon tafarki da kuma cimma sabon buri.
Fasahohin da Sin ta samu a cikin shekaru 100 da suka gabata sun karawa Sinawa karfi da tunani. Yayin da ake yin kokari wajen raya kasa ta zamani bisa tsarin gurguzu a dukkan fannoni da neman cimma babban buri na biyu yayin da Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ta cika shekaru 100 da kafuwa, shugaba Xi ya bayyana cewa, bai kamata a gamsu da nasarorin da aka samu a yanzu ba, akwai doguwar tafiya don samun zaman rayuwa mai karin jin dadi a tsakanin jama’a. (Zainab Zhang)