Tun daga ranar 5 zuwa ta 11 ga wannan wata, memban hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi yana ziyarar kasashe hudu a Afirka bisa gayyatar da aka yi masa.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin da Afirka suna sada zumunta na dogon lokaci, kasar Sin ta kiyaye sada zumunta da yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka. A ganin kasar Sin, ba a manta da nahiyar Afirka ba, saboda ya kasance yanki mai karfi da damar samun ci gaba. Nahiyar Afirka mai ci gaba za ta kara samar da gudummawa wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa a duk duniya baki daya.
Game da batun cika shekaru 30 da kafuwar hukumar cinikayya ta duniya wato WTO, Guo Jiakun ya bayyana cewa, yin cinikayya cikin ‘yanci bukatu ne na samun bunkasar tattalin arzikin duniya. Kasar Sin za ta ci gaba da bin ka’idojinta da aka tsara yayin da ta shiga hukumar WTO, da yin kokari tare da kasa da kasa wajen tabbatar da tsarin yin cinikayya a tsakanin bangarori daban daban bisa tushen hukumar WTO, da sa kaimi ga yin cinikayya da zuba jari cikin ‘yanci da sauki don kara amfanawa duniya baki daya.
Ban da wannan kuma, Guo Jiakun ya bayyana cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ta gabatar da ruhin Shanghai, ta hakan an bude sabon babi na raya huldar dake tsakanin kasa da kasa. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp