Dangane da rahotannin baya-bayan nan da kafafen yada labarai da dama suka bayar game da batutuwan bayyana bayanan sirri daban daban, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, batun tsaron yanar gizo batu ne na duniya baki daya, akwai bukatar kasa da kasa su yi hadin gwiwa wajen tinkarar batun, kiyaye tsaron yanar gizo wani nauyi ne da aka rataya a wuyan kasashen duniya.
Mao Ning ta bayyana cewa, Sin ta kasance mai tabbatar da tsaron yanar gizo. Sin ta ba da shawarar tabbatar da tsaron bayanai na duniya, don bayar da gudummawar Sin game da tsara ka’idojin tafiyar da bayanan sadarwa na duniya. Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa da kasashen duniya wajen gina yanayin yanar gizo mai zaman lafiya da tsaro da bude kofa da hadin gwiwa yadda ya kamata. (Zainab)