Bisa rahoton hada-hadar kudade da aka samu, da wadanda aka kashe tsakanin kasa da kasa na farkon rabin shekarar 2022 na kasar Sin, wanda hukumar kula da musayar kudade ta kasar Sin ta fitar a kwanakin baya, Sin ta kara zurfafa bude kofa ga kasashen waje, a karin yankuna da fannoni daban daban, wanda hakan ya sa kaimi ga kyautata tsarin Sin na zuba jari da tattara kudi a tsakanin kasa da kasa.
Rahoton ya bayyana cewa, tare da kyautata yanayin cininki a cikin kasar Sin, an samu kyakkyawar kasuwar kashe kudi a kasar, don haka kamfanonin kasa da kasa suka fi son zuba jari ko kafa kamfanoni a kasar Sin.
Rahoton ya nuna cewa, ya zuwa farkon rabin shekarar 2022, yawan jarin da kamfanonin kasashen waje suka zuba kai tsaye a kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 3.6, adadin da ya karu da kashi 73 cikin dari bisa na karshen shekarar 2012. Kana bunkasuwar karfin kamfanonin Sin, ta sa su fi bukatar fita waje, hakan ya sa yawan jarin da kamfanonin Sin suka zuba ga kasashen waje kai tsaye, ya karu daga dalar Amurka biliyan 500 a karshen shekarar 2012, zuwa dalar Amurka triliyan 2.6 a farkon shekarar 2022. (Zainab)