Mai magana da yawun kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da ketare ya amsa tambaya da manema labarai suka gabatar masa kan takardar bayani a kan manufar “Zuba jari a Amurka ta zamanto farko” a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya Lahadi. Inda ya ce, bangaren masana’antu da kasuwancin Sin na matukar kin yarda da matakin da Amurka ta dauka, wanda ya yi gamin-gambiza da batun tsaron kasa wuri guda, sannan ya yi hannu riga kwata-kwata da tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Kakakin ya kara da cewa, Amurka ta tsaurara matakan tsaro da nufin fakewa da guzuma ta harbi karsana a kan shigo da jari daga bangaren Sin a fannin kimiyya da manyan ababen rayuwa da kiwon lafiya da aikin gona da makamashi da kayayyakin da ake sarrafawa da sauransu, a hannu guda kuwa, ta yi yunkurin habaka takaita zuba jarinta a kasar Sin ta hanyar daukar matakan sanya takunkumi da tantance harkar kudade da sauransu. Kuma da zarar an aiwatar da matakan da ake dauka, za su kara tagayyara manufofin da kamfanoni za su aiwatar, zai yi matukar illa ga zaman oda da dokar cinikayyar duniya da haifar da rashin tabbaci ga tsarin samar da kayayyaki a duniya.
Kakakin ya ce, “Sin na kalubalantar Amurka da ta mutunta ka’idar kasuwanci da yin takara daidai wa daida, da kuma fahimtar ainihin iyakar batun tsaron kasar da soke kayyade zuba jari tsakanin kasashen biyu ta yadda za a shimfida yanayi mai yakini ga masana’antu da kasuwancin kasahen biyu kan hadin gwiwarsu ta moriyar juna.” (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp