Kakakin ma’aikatar kasuwanci na Sin, ya bayyana a jiya Juma’a cewa, a ranar 17 ga watan Afrilun bana, ofishin wakilin kasuwanci na Amurka, ya sanar da matakan karshe na bincike da ta gudanar bisa sharadi mai lamba 301 na Amurka a kan jiragen ruwa, da ayyukan sufuri da suka shafin kasar Sin, har ma jiragen ruwa da aka gina a kasar Sin. Kuma daga cikin wadannan matakai, harajin tashar jiragen ruwa da za a dorawa jiragen ruwan Sin zai fara aiki a ranar Talata 14 ga watan nan na Oktoba.
Kakakin ya ce, matakan da Amurka ta dauka, ba shakka ra’ayi ne na son kai, da bangaranci, kuma suna nuna wariya, wanda ke kawo matukar illa ga kamfanonin Sin. Don haka Sin ta nuna rashin jin dadi, da kin amincewa da hakan.
Jami’in ya kara da cewa, domin kare muradun masana’antu na cikin gida, hukumomin Sin za su kara haraji na musamman kan jiragen ruwan da ke da alaka da Amurka, bisa dokokin sufuri na kasa da kasa na jamhuriyar jama’ar Sin, wato kan wadanda ke kafa tutar Amurka, da wadanda aka gina a Amurka ko mallakin kamfanonin Amurka. Wadannan matakai za su fara aiki ne tun daga ranar Talata mai zuwa, lokacin da Amurka za ta fara aiwatar da harajin da ta sanya wa jiragen ruwan Sin. (Amina Xu)