An gudanar da bikin mika filayen wasa 4 da kasar Sin ta yi wa gyaran fuska kyauta ga kasar Senegal a jiya Juma’a, a filin wasa na Leopold Sedar Senghor dake birnin Dakar, fadar mulkin kasar.
Yayin bikin mika aikin, ministar matasa, wasanni da raya al’adu ta kasar Khady Diene Gaye, ta ce aikin daya ne daga cikin manyan ayyukan tallafi da kasar Sin ta gudanar a Senegal, wanda ta fara aiwatarwa tun daga farkon shekarar 2022, ya kuma kunshi kwaskwarima, da daga matsayin filin wasa na Senghor dake Dakar, da wasu kananan filayen wasan dake Kaolack, da Diourbel da Ziguinchor.
Minsitar ta ce, bikin kaddamarwa ba na mika aiki ne kadai ba, har ma ya zamo wani muhimmin lokaci na waiwaye game da dankon zumunta dake tsakanin Sin da Senegal. Tun kammala gininsa da tallafin gwamnatin kasar Sin a shekarun 1980, filin wasa na Senghor ya ci gaba da kasancewa gini dake alamta abota mai karfi tsakanin kasashen biyu. A yanzu kuma sakamakon zamanantar da shi, ya sauya zuwa gini mai kayatarwa. Godiya ga tallafin kasar Sin, da kwazon aikin tawagar Sin da ta Senegal bisa tabbatar da nasararsa. Gyaran fuskar ya kara kyautata kayayyakin bukata dake cikin filin wasan, tare da nuni ga karfin hadin gwiwar sassan biyu a fannin raya wasanni da al’adu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp