A cikin ‘yan kwanakin nan, rikicin dake tsakanin kasashen Indiya da Pakistan na ci gaba da karuwa. Pakistan ta ce, yau Asabar, Indiya ta kai hari ga sansanin sojojinta na sama da wasu wurare, kuma za ta mai da martani a kan hakan. Inda a halin yanzu, ita ma ta fara kaddamar da ayyukan farmakin soji.
Game da hakan, wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na mai da hankali kan halin da ake ciki tsakanin Indiya da Pakistan, kuma ta damu matuka da yadda wutar rikicin ke kara ruruwa.
- Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow
Kasar Sin ta yi kira ga kasashen na Indiya da Pakistan da su ba da fifiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankali, kowa ya mayar da wukarsa cikin kube, da komawa kan turbar warware sabaninsu ta hanyar siyasa cikin lumana, da kauce wa daukar matakan da za su kara tsananta rikicin.
Jami’in ya kara da cewa, wannan ya dace da muhimman muradun Indiya da Pakistan, kuma zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, sannan kuma shi ne fata na gama-gari na kasashen duniya. Kuma kasar Sin na son ci gaba da taka muhimmyar rawa mai ma’ana a wannan fanni. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp