Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayyana a yau Talata cewa, matakin da kungiyar tarayyar Turai (EU) ta dauka na shigar da kamfanoninta da wasu Sinawa a cikin shirin kakaba takunkumi na 16 a kan kasar Rasha, zai yi kafar ungulu ga huldar kasuwanci tsakanin sassan biyu.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya ce, matakin na EU ya saba wa yarjejeniyar da shugabannin bangarorin biyu suka cimma, inda ya bukaci kungiyar ta EU ta daina saka sunayen kamfanonin kasarta da Sinawa cikin takunkuman, kana ta guji bata suna da dora zargi a kan kasar Sin.
Kasar Sin ta yi imanin cewa, tattaunawa da yin shawarwari ne kawai hanyoyin da za a bi wajen warware rikicin kasar Ukraine, kuma tana goyon bayan shawarwarin zaman lafiya a ko da yaushe, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana, inda ya kara da cewa, kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace don kiyaye halaliya da muradun kamfanonin kasarta.
Bugu da kari, dangane da kakaba takunkumin da kungiyar EU ta yi a kan kamfanonin kasar Sin saboda samar da bayanan da suka shafi sararin samaniya da tauraron dan Adam ga kasar Rasha, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum a yau Talata 25 ga wata cewa, kasar Sin tana nan a kan bakanta na nuna adawa da haramtaccen takunkumin da aka kakaba ta hanyar kudin goro, kuma bai kamata a rika tsoma baki cikin harkokin mu’amala da hadin gwiwa da aka saba a tsakanin kamfanonin Sin da kasar Rasha ba, da kuma illata abin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp