Jiya ne, aka kammala taron shugabannin kungiyar kasashen yankin Asiya da Fasifik (APEC) karo na 29 a kasar Thailand. Taron ya zartas da muhimman takardun sakamako guda biyu, da sanarwar shugabannin APEC, da burin Bangkok na raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, wanda ke nuna manufofi da shawarwari da suka dace da kasar Sin.
Kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun yi imanin cewa, muhimmin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya kara haskaka “lokacin yankin Asiya” na tafiyar da harkokin duniya, kuma kasar Sin ta kasance jagora wajen hada kan dukkan sassa don tunkarar kalubaloli iri daya.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp