Mahukuntan kasar Sin sun ware kudade har yuan biliyan 5.27, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 733.5, domin tabbatar da hidimar dumama muhalli yayin hunturu ga mutanen da ibtila’i ya shafa.
Ma’aikatar kudin kasar ce ta bayyana hakan a Juma’ar nan, inda ta ce kudaden da aka ware sun fito ne daga ma’aikatar kudi da ta ayyukan gaggawa, kuma za a kashe su wajen tallafawa kananan hukumomi, don al’ummun yankunan da suka gamu da ibtila’i su samu isasshen dumi a lokacin hunturu da bazara, inda za a mayar da hankali sosai ga samar da yanayin rayuwa mai dadi gare su. (Mai fassara: Saminu Alhassan)