Yayin da ranar ma’aikatan kiyaye zaman lafiya ta MDD ke karatowa a ranar 29 ga wannan wata, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya Jean-Pierre François Renaud Lacroix ya bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, ya na alfahari sosai da yadda aka gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD har na tsawon shekaru 75, kana ya yabawa kasar Sin domin ta samar da muhimmiyar gudummawa kan sha’anin kiyaye zaman lafiya na MDD.
Jean-Pierre Lacroix ya ce, Sin ta kasance mai goyon bayan MDD wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, kana ta samar da gudummawa sosai ga ayyukan.
Yayin da Lacroix ya ke bayani game da nasarorin da aka samu wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, ya bayyana cewa, kasashe da dama sun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali sanadiyyar ayyukan kiyaye zaman lafiya, lamarin da ya shaida cewa, ayyukan suna da amfani.
Haka zalika Lacroix ya ce yana fatan a nan gaba, MDD da Sin za su kara hadin gwiwa kan ayyukan kiyaye zaman lafiya. (Zainab)