A yau ne hukumar bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa ta Sin, ta fitar da wani rahoto mai taken “Matakan zahiri da Sin ke aiwatarwa domin raya hadin gwiwar kasa da kasa”, rahoton da ya yi fashin baki game da tallafin jin kai na gaggawa, da wasu fannonin na daban, wadanda kasar ta bayar ga kasashen ketare cikin shekarun baya bayan nan.
Alkaluman dake kunshe cikin rahoton, da aka fitar a nan birnin Beijing, sun nuna cewa, tsakanin shekarar 2018 zuwa 2022, Sin ta samar da tallafin jin kai na gaggawa ga kasashen ketare da yawan su ya kai 822.
Kuma baya ga bangaren kayayyaki, da kudade da Sin din ke ba da tallafin su, a daya hannun kasar tana tura tawagogin aikin ceto, da kwararru a fannin kiwon lafiya zuwa kasashen dake cikin yanayi na bukata, wanda hakan ya fadada hanyoyin tallafin na Sin.
Kaza lika rahoton ya nuna cewa, a cikin shekaru ukun da suka shude, Sin ta samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 har biliyan 2.2 ga sama da kasashe da hukumomin kasa da kasa 120 dake sassan duniya daban daban, wanda hakan ya samar da babbar gudummawa ga bukatar da sassan duniya ke da ita ta rigakafi mai sauki, da musamman ma kasashe masu tasowa. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)