Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi bayani game da nasarorin da Sin ta cimma, a cikin shekaru 60 da ta shafe tana samarwa kasashen waje tallafin kiwon lafiya, inda ya ce a tsawon shekarun 60, Sin ta samarwa kasashen waje hidimomin kiwon lafiya ta hanyar tura likitoci, don samar da gudummawa ga abokan ta, ba tare da sharudan siyasa ba, kana ba tare da neman wata moriya ba, kuma wannan hulda ce da za ta wanzu a dogon lokaci.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, bayan da kasar Sin ta tura tawagar likitoci ta rukunin farko zuwa kasar Algeria a watan Afrilu na shekarar 1963, ta kara tura likitoci har adadin ya kai dubu 30 ga kasashe da yankuna 76 na duniya, wadanda suka bada jinya ga marasa lafiya miliyan 290.
Har ila yau, Sin za ta ci gaba da tura likitocin ta zuwa kasashen waje, don gudanar da ayyukan kiwon lafiyar al’umma, da samar da moriya ga jama’ar kasashe masu tasowa, ta yadda za a cimma burin kiwon lafiyar dukkanin bil Adam, bisa tsarin bai daya. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp