Ma’aikatar kula da sashen ayyukan jigilar kayayyaki ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, a cikin rabin farkon bana, an samu ci gaba mai yawa a bangaren, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a jiya Lahadi.
Hukumar raya ci gaban kasa da gudanar da gyare-gyare, wacce take da alhakin tsara tsare-tsaren tattalin arzikin kasa ta yi bayanin cewa, kudin da ake kashewa a ayyukan jigilar kaya ya kai kaso 14 cikin dari na GDPn kasar a watanni shida na farkon shekarar, inda ya ragu da kaso 0.1 cikin dari idan aka misalta da na rubu’in farko, kuma ya ragu da kashi 0.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
A cewar hukumar, wannan na nuni ne da sakamakon farko da aka samu wajen rage tsadar ayyukan a cikin al’umma. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp