Mai magana da yawun ma’aikatar kula da halittu da muhalli ta kasar Sin Pei Xiaofei, ya bayyana cewa, ingancin iska da ruwa a kasar Sin ya ci gaba da karuwa a rabin farko na shekarar shekarar 2025.
A yayin wani taron manema labarai da ya gudana a yau Litinin, Pei ya bayyana cewa, adadin kwanakin da aka samu iska mai ni’ima a biranen kasar Sin a matakin da ake so ko sama da haka ya kai kashi 83.8 cikin dari a tsakanin wannan lokaci, wanda ya karu da kashi 1 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
A halin da ake ciki kuma, adadin manyan tafkuna da ma’ajiyoyin ruwa da ake sa ido kan ingancin ruwa da ke kasa da matakin tantance lafiyarsa, watau Grade V, wanda yake mafi kankantar matakan tabbatar da ingancin ruwa mai hawa biyar na kasar, ya koma kashi 3.8 cikin dari, inda hakan ya nuna an samu raguwar kashi 0.5 cikin dari a wannan bangaren idan aka kwatanta da adadin na shekarar 2024. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp