Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce adadin karuwar mazauna biranen kasar ya fadada daga kaso 55.52 bisa dari a karshen shekarar 1949, zuwa kaso 66.16 bisa dari a karshen shekarar 2023.
Rahoton da hukumar ta fitar a Litinin din nan, ya nuna cewa cikin shekaru 75 da suka gabata, tun bayan kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, kasar ta gamu da manyan sauye sauye na gaggauta bunkasar birane a tarihin duniya.
Rahoton ya ce, ya zuwa karshen shekarar 1949, kasar Sin na da birane 129 ne kacal, wadanda ke da adadin mutane miliyan 39.49. Yayin da ya zuwa karshen shekarar bara, adadin biranen kasar ya kai 694, kuma mazauna manyan biranen kasar suka kai mutane miliyan 673.13. (Mai fassara: Saminu Alhassan)