A karon farko kwararrun likitocin kasar Sin sun yi nasarar dasa huhun alade da aka sauya kwayoyin halittarsa a jikin wani mutum. Wata makala mai kunshe da binciken kimiyya da aka wallafa a mujallar “Nature” ce ta tabbatar da hakan, inda bayanan suka nuna cewa, duk da kasancewar huhu bangaren jiki mai sarkakiya, amma likitocin da suka yi aikin sun cimma nasarar da ake ganin mataki ne na kaiwa ga gwajin aikin nan gaba ga marasa lafiya dake da bukata.
An ce wanda aka yiwa dashen huhun matashi ne mai shekaru 39 a duniya, wanda kwakwalwarsa ta riga ta mutu, kuma an yiwa huhun na alade sauye-sauyen yanayin halitta shida, domin ya dace da yanayin jikin dan’adam kafin dasawa mara lafiyan. Daga bisani likitocin da suka yi aikin sun ce mara lafiyan ya shafe kwanaki tara jikinsa na aiki da huhun, ba tare da jikinsa ya bijirewa huhun ko ya kamu da wata cuta ba.
Daya daga mawallafa binciken He Jianxing, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sakamakon karuwar bukatar dashen sassan jiki a duniya, dabarar dashen wasu sassan jikin wasu halittu a jikin bil’adama na iya zama hanyar magance matsalar karancin sassan jiki da wasu ke bayarwa domin dasawa marasa lafiya. Ya ce nasarar da aka cimma a wannan karo ta zamo muhimmin mafari a fannin dashen sassan jikin wasu halittu ga marasa lafiya. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp