A ci gaba da shirye-shiryen bikin ciki shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin jinin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, majalisar gudanarwar kasar Sin ta sanar da tabbatar da rukuni na hudu na abubuwa da wurare 34, don tunawa da yakin kin jinin mamayar dakarun Japan a matakin kasa. A nata bangare kuma, ma’aikatar lura da harkokin da suka shafi tsofaffin sojoji ta kasar Sin, ta fitar da sanarwa mai kunshe da bayanai, game da ayyana rukuni na hudu na wasu shahararrun jarumai da gungun jarumai 43 da suka sadaukar da ransu, yayin yakin kin jinin mamayar dakarun Japan.
Sanawar da ta fito daga majalisar gudanarwar kasar Sin, ta shaida cewa ya wajaba dukkanin yankunan kasar, da sassan hukumomi masu ruwa da tsaki su karfafa kariya, da kula da abubuwa da wurare masu tunatarwa game da yakin kin jinin mamayar dakarun Japan, kana a yi aiki bisa tsanaki wajen tonowa, da rarrabewa, da yayatawa, da baje kolin abubuwan tarihi, da na al’adu, da ayyukan ’yan mazan jiya masu nasaba da batun.
Sa’an nan a dage wajen yayata ruhin kishin kasa, da na yakin kin jinin mamayar dakarun Japan, da bunkasa manufar dunkulewar kasa waje guda. (Saminu Alhassan)