Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Saliyo, wajen aiwatar da muhimmiyar matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa kawance, da amincewa da goyon bayan juna.
Liu, ya yi tsokacin ne a jiya Juma’a, yayin ganawarsa da mataimakin shugaban kasar Saliyo Mohamed Juldeh Jalloh, a bangaren ziyarar aiki da ya gudanar a kasar ta Saliyo, tsakanin ranakun Laraba zuwa jiya Juma’a.
Mataimakin firaministan na Sin, ya yi kira ga sassan biyu da su yi amfani da damar manufar nan ta kawar da haraji, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ta yadda za su kyautata karko, da ingancin hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, musamman a fannin noma da kamun kifi.
Liu Guozhong ya kara da cewa, a gabar da ake cika shekaru 10 da fara gabatar da tallafin kasar Sin, wanda ya haifar da nasarar shawo kan annobar Ebola a nahiyar Afirka, kamata ya yi Sin da Saliyo su ci gaba da zurfafa hadin kai a fannin kiwon lafiyar al’umma, domin cin gajiyar jama’arsu.
A nasa tsokaci kuwa, mista Jalloh jinjinawa kasar Sin ya yi dangane da tallafi mai ma’ana da ta rika bayarwa, yayin da ake fama da annobar Ebola, yana mai cewa, Saliyo za ta ci gaba da martaba manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, a fannin gina shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, da ingiza aiwatar da matakan hadin kai 10, da aka sanar a shekarar 2024 da ta gabata, yayin taron birnin Beijing, na tattauna hadin kan Sin da kasashen Afirka ko FOCAC, ta yadda za a kai ga cimma sabbin nasarori. (Saminu Alhassan)














