Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Zhang Xiaogang, ya ce Sin ta yi Allah wadai da kutsen da wani jirgin fasinja na kasar Japan ya yi a sararin samaniyar tsibirin Diaoyu Dao, yana mai jaddada cewa yankin mallakin kasar Sin ne, kuma wajibi ne Japan ta dakatar da aiwatar da matakan da ka iya haifar da tashin hankali da illata alakar kasashen biyu.
Zhang Xiaogang, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da batun, inda ya yi watsi da ikirarin Japan, cewa wai wani jirgi mai saukar ungulu na Sin ya keta sararin samaniyar kasar, yana mai cewa, wannan zargi ne marar tushe wanda ya sabawa gaskiya.
- Maniyyata Daga Turai Akan Dawakai Sun Isa Kasar Saudiyya Domin Yin Aikin Hajjin 2025
- Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?
Ya ce tsibirin Diaoyu Dao, da tsibiran dake kewayensa mallakin kasar Sin ne, kuma kutsen da jirgin fasinja na Japan ya yi a tsibirin ya yi matukar keta hurumin kare yankunan kasar Sin.
Jami’in ya kara da cewa, dakarun tsaron yankunan teku na Sin sun aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba, na gargadi da korar jirgin saman na Japan, wanda hakan mataki ne halastacce da kuma ya dace da doka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp