Kasar Sin ta sake nanata goyon bayanta ga kafa ‘yantattun kasashe biyu a matsayin sahihiyar hanyar warware rikicin Isra’ila da Palasdinu da yaki ci yaki cinyewa.
Wakilin kasar Sin a kungiyar kasashen Larabawa, Liao Liqiang ne ya bayyana haka, lokacin da yake jawabi ga taro na 4 na kawancen kasashen duniya domin aiwatar da shawarar kafa kasashe biyu, wanda ya gudana a birnin Cairo na kasar Masar.
- Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Bashin Albashin Ma’aikatan Tsaftar Muhalli 2,369
- Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Sabuwar Rundunar Tsaro A Jihar
Liao Liqiang, ya bayyana matukar damuwa game da yanayin da Gaza ke ciki tare da kira ga kasashen duniya su ingiza aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Wata sanarwar da ofishin jakadancin kasar Sin ya fitar, ta ruwaito Liao Liqiang na jaddada cewa, Gaza wani muhimmin bangare ne na yankin Palasdinu kuma ya kamata duk tsare-tsaren da ya jibanci makomarsa ya girmama muradun Palasdinawa da dokokin kasa da kasa da kudurorin MDD tare da la’akari da damuwar kasashen yankin.
Taron ya tattauna kan rawar da hukumar bayar da agajin jin kai ga Palasdinawa ta MDD (UNRWA) ke takawa da kuma takunkuman da Isra’ila ta sanya mata. Jakadan na kasar Sin ya nanata goyon bayan Sin ga ayyukan hukumar bayan kawo karshen rikicin Gaza, yana cewa, duk wani mataki da zai kawo tsaiko ga ayyukan hukumar, zai yi mummunan tasiri ga warware rikicin a siyasance. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)