Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Uganda, da hadin gwiwar wasu kamfanonin Sin dake kasar, da tawagar jami’an lafiya na Sin dake kasar, sun mikawa asibitin sada zumunta na Sin da Uganda kayayyakin aiki, wadanda za su taimaka wajen yaki da anobar COVID-19, da kuma cutar Ebola da ta barke a kasar.
Karamar Jakadar Sin dake Uganda mai kula da aikin kasuwanci, Madam Jiang Jiqing, da jami’in ofishin kasuwanci na ofishin jakadancin, su ne suka mika tallafin ga daraktan asibitin na sada zumunta Mr. Emmanuel Tugaineyo.
Cikin jawabin da ta gabatar a taron na ranar Alhamis, Madam Jiang ta jinjinawa alakar dake tsakanin Sin da kasar Uganda, tana mai cewa, kasashen 2 sun jima suna cudanya a fannin kiwon lafiya. Kuma tun daga shekarar 1983, kasar Sin ke ta aikewa da tawagogin kiwon lafiya zuwa Uganda, domin yada ilimi da sanin makamar aiki tare da jami’an lafiyar Uganda, baya ga jinyar da likitocin Sin ke baiwa al’ummar Uganda kai tsaye.
A nasa tsokaci yayin karbar kayan tallafin, Mr. Rony Bahatungire, wanda ya wakilci babbar sakatariyar ma’aikatar lafiyar kasar Diana Atwine, ya jinjinawa kasar Sin, bisa yadda yake martaba kawancen sassan biyu, musamman ta fuskar kiwon lafiya.
Bahatungire ya kara da cewa, Sin ta himmatu wajen tallafawa kasar Uganda, ta fuskar fadada asibitin, ta yadda zai kunshi cibiyar masu fama da damuwa, wadda za ta amfani al’ummun Uganda da ma na kasashe makwaftan kasar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp