Alal hakika tarihi ba wai jerin bayanai ne kadai dake fayyace abubuwan da suka wakana a baya ba. Tarihi ya kunshi tarin darussa, kuma madubi ne na hangen nesa, kana manuniya game da inda aka dosa.
A jiya Laraba, kasar Sin ta gudanar da kasaitaccen biki na tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, kuma cikin jawabinsa shugaban kasar Xi Jinping ya bayyace yadda wannan rana ta kasance ta tunawa da juriyar da kasar Sin ta yi da mummunan yanayi na yaki, da yadda ranar ya kamata ta zama ta yin waiwaye adon tafiya, tare da jaddada aniyar kasar Sin ta ci gaba da nacewa bangaren gaskiya da adalci a tarihi, da ma goyon bayan duk wasu fannoni na bunkasa ci gaban rayuwar bil’adama.
Karkashin hakan, kasar Sin ta shafe tsawon lokaci tana bin tafarkin samar da ci gaban kanta, da ma bayar da gudummawar ci gaban duniya bisa turbar lumana, tana hada karfi da karfe da sauran sassan kasa da kasa, a kokarinta na gina duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama.
A yanzu haka, bayan shekaru 80 da cimma nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, ma iya cewa tarihi ya koyar da mu cewa gaskiya, da zaman lafiya, da zamantakewar bil’adama za su dore tare.
A yanzu da duniya ke fuskantar yanayi na tangal-tangal, tarihi ya koyar da mu cewa dole ne a kai zuciya nesa, a yi aiki da tunani mai zurfi, da sanin ya kamata wajen daukar matakai, ta yadda za a kiyaye sake maimaituwar mummunan tashin hankali. Tarihi ya nuna mana muhimmancin dagewa kan manufar wanzar da zaman lafiya ta hanyar sadaukarwa, kuma kasar Sin ta koyarwa duniya alfanun juriya da turjewa dannayi, wanda hakan ne ya kai ta ga cimma manyan nasarori masu ban mamaki, tun bayan kammala yakin duniya har kawo wannan lokaci. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp