Ma’aikatar kudi da ma’aikatar madatsar ruwa na kasar Sin sun bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin ta ware yuan biliyan 1, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 139.69, don daidaita asarar da aka yi a yankunan kogin Haihe da suka yi fama da bala’in ambaliyar ruwa a baya-bayan nan.
Za a yi amfani da kudin don biyan diyya ga asarar dukiyoyi na mazauna wadannan yankuna, da suka hada da lalacewar amfanin gona, filayen kiwon dabbobi da kaji, dazuzzuka na kasuwanci, gidaje da injunan noma, don taimaka musu fara aiki da rayuwa cikin gaggawa, in ji ma’aikatun. (Mai fassara: Yahaya)