• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Yanke Shawarar Kakaba Takunkumi Ga Kamfanonin Tsaron Amurka Guda Biyar

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta yanke shawarar sanya takunkumi ga kamfanonin tsaron Amurka guda biyar.

A baya-bayan nan ne Amurka ta sanar da sayar wa yankin Taiwan na kasar Sin sabbin makamai tare da sanya wa ‘yan kasuwa da wasu Sinawa takunkumi, bisa wasu dalilai marasa tushe. Kakakin ya sanar da matakin ne lokacin da aka tambaye shi game da matakan da Sin ke dauka kan wannan batu.

  • Jarin Da Sin Ta Zuba A Bangaren Sufuri Ya Karu A Cikin Watanni 11 Na Farkon 2023
  • Majalisar Gudanarwar Sin Ta Yi Kira Da A Kara Bunkasa Tsarin Kula Da Tsoffi

A cewar kakakin, yadda Amurka ta sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin makamai, ya saba wa manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwoyi guda uku da sassan biyu suka sanyawa hannu, musamman ma sanarwar hadin gwiwa ta ranar 17 ga watan Agustan shekarar 1982, da takunkumin da Amurka ta kakaba wa kamfanoni da daidaikun Sinawa bisa ka’idojin karya daban-daban, kuma suna yin illa sosai ga diyaucin da ma moriyar tsaron kasar.

Bugu da kari, cinikin makamai da takunkumin da Amurka ta kakaba ba bisa ka’ida ba, sun kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, da keta ‘yanci da halastattun hakkoki da muradun kamfanoni da daidaikun jama’a. Don haka, kasar Sin tana kakkausar suka da nuna adawa da hakan, ta kuma gabatar da kokenta ga kasar Amurka.

Ya bayyana cewa, a matsayin mayar da martani ga wadannan munanan ayyuka na kuskure da Amurka ta dauka, kuma bisa ga dokar yaki da sanya takunkumai na kasar Sin, kasar Sin ta yanke shawarar kakaba takunkumi ga kamfanonin tsaron Amurka guda biyar, wato BAE Systems Land and Armament,da Alliant Techsystems Operation, da Aero Vironment, da ViaSat, da kuma Data Link Solutions.(Ibrahim)

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Tinubu Ya Bada Umarnin Binciken Ma’aikatar Jin Kai Kan Zargin Karkatar Da Miliyan N585

Tinubu Ya Bada Umarnin Binciken Ma’aikatar Jin Kai Kan Zargin Karkatar Da Miliyan N585

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.