Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Geng Shuang, ya yi Allah wadai da hare-haren da sojojin Isra’ila ke kaiwa kasar Syria.
Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya Alhamis, a gun taron gaggawa na kwamitin sulhu na MDD kan batun Syria. Yana mai cewa, a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula a kudancin Syria, a baya-bayan nan Isra’ila ta kai hare-hare ta sama a Suwayda, Deraa, Damascus da sauran wurare, har ma da wasu muhimman “hukumomin gwamnati” a Syria.
Ya ce matakin na Isra’ila ya saba wa dokokin kasa da kasa, da cin zarafi ikon mulkin kasa da tsaro da cikakken ikon Syria na mallakar yankuna, da kuma kawo sabbin abubuwa masu sarkakiya ga zaman lafiya, kwanciyar hankali da mika mulki a Syria, kuma Sin tana Allah wadai da hakan a fili. Haka kuma tana kira ga Isra’ila da ta gaggauta dakatar da hare-haren da take kai wa kasar Syria, ta kuma janye jikinta daga yankin Syria cikin gaggawa.
Geng Shuang ya kara da cewa, a matsayin cibiyar dake da alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, ya kamata kwamitin sulhun ya tabbatar da ikon kundin tsarin mulkin MDD, da sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, da kuma yin aiki tukuru wajen sa kaimi ga warware rikice-rikicen, da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan da abin ya shafa, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya. Bugu da kari, ya ce a shirye Sin take ta yi aiki tare da kasashen duniya don taka rawar gani a wannan fanni. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp