Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce tsakanin watan Janairu zuwa Satumban shekarar nan ta 2024, adadin kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a sassan kasar, sun kai 42,108, yayin da darajar jarin waje da aka yi amfani da shi a cikin kasar ya kai yuan biliyan 640.6.
Kaza lika, rahotanni daga ma’aikatar sun nuna karuwar hada hadar cinikayyar hajojin sari, da na sayayyar daidai, tun daga farkon shekarar ta bana.
A wani ci gaban kuma, alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin, sun nuna yadda tsakanin watan na Janairu zuwa Satumba, karuwar darajar hajojin kamfanoni dake samar da hajojin sari da na sayayyar daidai, ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 9.4, karuwar da ta kai ta kaso 5.4 bisa dari a shekara guda. (Mai fassara: Saminu Alhassan)