Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing, ya ba da jawabi a taron tattaunawa kan batun Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya wato CAR, wanda kwamitin sulhun MDD ya kira a jiya Talata, inda ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan gamayyar kasa da kasa za su nuna goyon baya ga kasar Afirka ta Tsakiya, wajen gaggauta yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar.
Dai Bing ya ce, an samu gagarumin ci gaba a yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar, kuma kasar Sin tana fatan gamayyar kasa da kasa za su ba da goyon bayana a ayyukan fasahohi, da na kudade ga kasar, ta yadda za ta iya gaggauta gudanar da zabe, da shimfida zaman lafiya.
Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kokarin da gwamnatin Afirka ta Tsakiya take yi wajen tabbatar da kwanciyar hankali a kasar, da kiyaye tsaron al’ummominta. Kana za ta goyi bayan kasar wajen karfafa tsaro a kan iyaka.
Daga nan sai ya yi kira ga kwamitin sulhu na MDD, da ya saurari bukatun kasar Afirka ta Tsakiya, da kuma kasashen da rikicin ta ya shafa, domin kawar da matakan da ba su dace ba, da kuma kawar da takunkumin da aka kakabawa kasar bisa dukkan fannoni. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)