Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi fatan Amurka za ta dakatar da yunkurin da take yi na neman zama madaukakiya, kana ta natsu wajen sauraren muryoyin sassan kasa da kasa.
Wang Yi, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron hadin gwiwa na ganawa da ‘yan jaridu, bayan zantawa da takwararsa ta kasar Indonesia Retno Marsudi.
Ya ce, ya kamata jami’an kasar Amurka su yi nazari a fannin ilimin dokokin kasa da kasa tabbatattu. Wang ya ce, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashe mambobin kungiyar yankin kudu maso gabashin Asiya, a fannin aiwatar da yarjejeniyar gudanar da cudanya a tekun kudancin Sin, da ingiza tattaunawa game da tsare-tsaren aiwatar da harkoki a yankin tekun kudancin Sin, ta yadda za a gina shi ya zama mai yanayin zaman lafiya da hadin gwiwa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp