Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce Sin na fatan gwamnatin Amurka za ta yi aiki tare da bangaren Sin wajen kyautata fahimtar juna, da rage sabani, da karfafa hadin gwiwa ta hanyar gudanar da shawarwari da tattaunawa.
Guo Jiakun, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum, lokacin da yake amsa tambaya game da batutuwan da suka shafi alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, ya ce matsayar kasar Sin game da batutuwan karin haraji a bayyane take kuma ba ta sauya ba.
Ya ce, “Muna fatan Amurka za ta yi aiki tare da Sin, wajen aiwatar da muhimmiyar matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin zantawarsu ta wayar tarho, tare da taka rawar gani wajen tabbatar da nasarar tsarin shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu.”
Daga nan sai jami’in ya yi kira ga Amurka da ta yi aiki tare da bangaren Sin, wajen ingiza daidaito, da alakar samar da ci gaba mai inganci, da dorewa tsakanin sassan biyu. (Saminu Alhassan)