A jiya ne, mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Geng Shuang ya yi kira ga kasa da kasa da su taimakawa kasashe masu fama da rikici wajen daukar matakai don kawar da yunwa da talauci, da ba da ilmi da kiwon lafiya, ta haka za a tabbatar da rayuwar yaransu a dukkan fannoni.
Geng Shuang ya bayyana a gun taron kwamitin sulhun MDD kan huldar dake tsakanin yara da rikici cewa, ya zuwa yanzu yara miliyan 150 a duk duniya suna bukatar aikin jin kai, tabbatar da aikin jin kai da shigar da kayayyakin jin kai ba tare da matsala ba, tushe ne na tabbatar da moriyar wadannan yara. Sin tana fatan kasa da kasa da kwamitin sulhun MDD za su dauki matakai don kawar da cikas ga aikin jin kai, da nuna goyon baya da tabbatar da rayuwar dukkan yara da suke fuskantar rikici.
Geng Shuang ya kara da cewa, MDD za ta gudanar da taron koli na nuna makoma a watan Satumba na bana. Ya kamata kasa da kasa su yi amfani da wannan dama don sa kaimi ga tsara taswirar raya yara da gabatar da tsare-tsare masu dacewa don amfanawa yara da tabbatar da tsaronsu da samar da kyakkyawar makomarsu a nan gaba. (Zainab Zhang)