Jakadan kasar Sin a MDD Wang Hongbo, ya yi kira ga kasa da kasa da su hada kai tare da kara samar da agajin jin kai ga yankin kahon Afrika.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ruwaito Wang Hongbo na yin kiran ne yayin wani taro kan tunkarar matsalolin agajin jin kai da ya gudana ranar Laraba, domin shawo kan tasirin rikicin Ukraine da ma takunkumai masu alaka da samar da abinci a Afrika.
Jakadan na kasar Sin ya ce a matsayinta na aminiya kuma abokiyar huldar kasashen yankin kahon Afrika, kasar Sin na daukar matsaloli na gajeren zango da ma bukatu masu dogon zango na kasashen yankin da muhimmanci, kuma tana iyakar kokarinta wajen taimaka musu tunkarar kalubalen agajin jin kai. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp