An cimma kunshin yarjejeniyoyin sauyin yanayi a ranar 24 ga wata a gun taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 29 wato COP 29, a birnin Baku na kasar Azerbaijan. Yarjejeniyoyin sun hada da shawarwari kan sabuwar manufar ba da kudade daga rukunoni kan harkokin da suka shafi yanayi wato NCQG, da batutuwan da suka shafi tsarin kasuwancin carbon na duniya a karkashin sashe na 6 na yarjejeniyar Paris.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labarai na yau 25 ga wata cewa, sakamakon taron ya nuna ka’idar “ana tare a zahiri amma an sha bamban a daukar alhaki”, kana ya nuna kokarin hadin gwiwa da kuma aniyar duniya wajen tinkarar sauyin yanayi.
Mao ta kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga kasashen da suka ci gaba da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na bayar da tallafin kudin magance sauyin yanayi ga kasashe masu tasowa, da kuma ba da gudummawa wajen aiwatar da ayyukan duniya kan daidaita sauyin yanayi. Hakazalika, Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, da ba da taimako gwargwadon karfinta ga sauran kasashe masu tasowa, wajen tinkarar sauyin yanayi. (Mohammed Yahaya)