Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, kasar Sin tana kira ga kasashen duniya da su hada kai, don hana rikicin Falasdinu da Isra’ila kara fadada.
Rahotanni na cewa, a kwanan nan Isra’ila ta kafa majalisar ministocin kula da yaki, ta kuma bukaci mazauna yankin arewacin zirin Gaza su miliyan 1.1 da su koma kudancin zirin cikin sa’o’i 24.
- Sin Da Saudiyya Na Hadin Gwiwar Gina Sabon Birnin Red Sea Karkashin Hadin Gwiwar Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya
- Alkaluman Awon Sauyin Tsadar Kayayyaki Da Na Hidimomi Na Kasar Sin Ba Su Sauya Ba A Watan Satumba
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira da kakkausar murya ga Isra’ila da ta janye matakin korar da ta dauka kan mazauna arewacin zirin Gaza.
Kan wannan batu, Wang Wenbin ya ce, kasar Sin tana adawa da duk wani abu da ke iya cutar da fararen hula da kuma saba wa dokokin kasa da kasa, kuma tana goyon bayan MDD wajen taka muhimmiyar rawa wajen hana ci gaba da fadadar al’amura, da kiyaye dokokin jin kai na kasa da kasa.
A ‘yan kwanakin nan, manzon musamman na gwamnatin kasar Sin kan batun yankin Gabas ta Tsakiya Zhai Jun, ya tattauna ta wayar tarho da jami’an ma’aikatun harkokin wajen Falasdinu, da Isra’ila, da Masar, da Saudiyya da sauran kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, domin yin shawarwari da dukkan bangarori kan tashin hankalin dake faruwa a halin yanzu tsakanin Falasdinu da Isra’ila. A game da haka, Wang Wenbin ya gabatar da cewa, Zhai Jun ya jaddada a cikin wata tattaunawa ta wayar tarho cewa, hanya mafi dacewa ta warware rikicin Palasdinu da Isra’ila ita ce a koma kan “matsayin kafa kasashe biyu”, da dawo da shawarwarin zaman lafiya, da kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, da tabbatar da zaman jituwa tsakanin Falasdinu da Isra’ila. Don haka, ya kamata kasashen duniya su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na samar da yanayi na sake fara shirin tabbatar da zaman lafiya.(Ibrahim)