Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na maraba da amincewar da babban taron MDD ko UNGA karo na 79 ya yi, da kudurin da ta gabatar, bisa jigon “Ingiza hadin gwiwar kasa da kasa a fannin amfani da dukkanin matakai don zaman lafiya, karkashin manufofin tabbatar da tsaron kasa da kasa”.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai na Talatar nan da ya gudana a birnin Beijing, lokacin da aka nemi ya yi karin haske game da batun, ya ce bisa tushen daidaito wajen shiga a dama da kowa, kudirin na da burin ganin an karfafa rawar da MDD ke takawa, a fannin ingiza shawarwari da hadin gwiwa, da kare halastattun muradu da moriyar kasashe masu tasowa, musamman wadanda suka jibanci amfani da kimiyya da fasaha ta hanyoyin zaman lafiya.
Kaza lika, kudurin ya nemi wasu kasashe da su dakatar da keta hurumin ka’idojin fitar da hajoji, da aiwatar da matakai marasa dacewa da doka, da daukar matsaya ta bangare guda, da gallazawa sauran sassa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)