Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce Sin na maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan. Guo wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, ya ce Sin na matukar fata, da goyon bayan dorewar tattaunawa da shawarwari tsakanin kasashen biyu, ta yadda za su kai ga shawo kan bambance-bambancensu, da cimma cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai dorewa, tare da hada karfi wajen kare zaman lafiya da daidaito tsakanin kasashen biyu da ma yankin da suke.
Game da batun sufurin jiragen kasa masu saurin gaske kan layin dogo na Jakarta zuwa Bandung na kasar Indonesiya ko HSR, Guo Jiakun ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da bangaren Indonesiya, wajen ci gaba da cin gajiyar sufurin jiragen kasar na HSR, da ingiza cikakkiyar gudunmawar aikin, wajen bunkasa tattalin arzikin Indonesiya, da raya zamantakewar al’ummarta, da hade sassan yankin da kasar take.
Dangane da kiraye-kirayen baya-bayan nan daga wasu ‘yan kasar Paraguay, masu bukatar a shiga tattaunawa mai ma’ana da fadi, don lalubo hanyoyin kulla dangantakar diflomasiyya da cinikayya tsakanin kasar da Sin, Guo ya ce abu mafi dacewa a yi shi ne a rungumi manufar Sin daya tak a duniya. Ya ce wannan ne batu da tarihi ya wanzar, kuma ya dace da ra’ayoyin jama’a. Jami’in ya kara da kira ga wasu tsirarun kasashe ciki har da Paraguay, da su yi duba na tsanaki, su saurari ra’ayoyin masu hangen nesa, kar su kawar da kai daga burin al’ummunsu, kana su gaggauta zabar matakin siyasa na gari, wanda zai haifar da cimma nasarar moriyar al’ummun kasashen cikin dogon lokaci. (Saminu Alhassan)