Na’urar zirga-zirgar sararin samaniya kirar kasar Sin da aka yi gwajin sake amfani da ita ta sauka a wurin da aka tsara cikin nasara a yau Litinin 8 ga wannan wata a cibiyar harba tauraron dan Adama dake Jiuquan na lardin Gansu na kasar, bayan da ta yi zirga-zirga a sararin samaniya bisa falaki da tsawon kwanaki 276.
Nasarar gwajin da aka cimma ta alamta cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako kan aikin nazarin fasahar kera na’urar zirga-zirgar sararin samaniya da ake iya sake amfani da ita, kuma za ta samar da dabara mai sauki da araha ga kasa da kasa yayin da suke amfani da sararin samaniya cikin lumana. (Mai fassarwa: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp