A yau Litinin ne masana kimiyya suka sanar cewa, kasar Sin ta yi nasarar kirkirar kwayar halittar shanun Zhangmu da na Apeijiaza, wasu nau’ikan shanu guda biyu wadanda ke cikin hadarin bacewa daga doran kasa da aka samu a yankin Xizang dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Kwanan nan ne aka haifi ‘yan maruka hudu na nau’o’in guda biyu a gundumar Yunyang da ke kudu maso yammacin birnin Chongqing na kasar Sin, ta hanyar kirkirar kwayar halittarsu, wanda ya zama karon farko a duniya da aka yi nasarar kirkirar kwayar halittar shanu daga Xizang. (Mai fassara: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp