Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta damu matuka kan yadda Amurka ta ba da umarnin sake duba yadda ake zuba jari a kasashen waje, kana Sin na da ikon mayar da martani.
Kakakin ya kara da cewa, Sin na fatan kasar Amurka za ta mutunta dokokin yanayin da kasuwa ke ciki da ka’idar yin takara ta gaskiya.
Haka zakila ma, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana Alhamis din nan cewa, kasar Sin ta nuna rashin gamsuwa matuka da ma adawa da nacewar kasar Amurka, na bullo da matakan takaita zuba jari a kasar Sin, ta kuma gabatar da rashin amincewarta ga bangaren Amurka kan wadannan matakai marasa dacewa. (Ibrahim)