A yau ranar 21 ga wannan wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, batun nukiliya na kasar Iran yana da nasaba da zaman lafiya da tsaro na yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na duniya. Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan daidaita batun nukiliya na kasar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya cikin lumana, wannan ita ce kwakkwarar hanyar da ta dace. Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi hadin gwiwa don sa kaimi ga koma kan hanyar siyasa.
Game da halin da zirin Gaza yake ciki kuwa, Guo Jiakun ya bayyana cewa, kasar Sin ta mai da hankali ga yanayin da ake ciki a zirin Gaza, da kin amincewa da duk wani yunkuri na kawo barazana ga fararen hula da saba wa dokokin kasa da kasa. Guo Jiakun ya yi nuni da cewa, bai kamata a kai hari ga fararen hula ba, kuma bai kamata a kawo barazana ga tsaron masu aikin jin kai ba, Sin tana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su tsagaita bude wuta cikin hanzari, da kawo karshen rikicin, da kuma sassauta yanayin jin kai a zirin. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp